Hotunan yadda Macizai ke jima'a da yadda suke haihuwa

Isyaku Garba | 23-7-2019 |


Macizai sukan sadu ne bayan maciji miji da macijiya mace sun hade waje daya ta hanyar laulaye jikinsu daga farkon kai har zuwa wutsiya, jela ko bundi inji Sakwatawa. Ta hakan ne macizan za su yi ta laulayewa  har maciji ya sami daidaita al'aurarsa da na mace, kafin ya saki maniyi.


Ba kamar 'yan adam ba, macijiya tana iya kin daukar ciki idan har bata son cikin, ko da bayan sun gama saduwa da maciji ne..


Saduwa na jima'i tsakanin macizai yakan dauki akalla awa daya, wani lokaci kasa da awa daya, haka zalika mafi yawan lokaci yakan dauki kusan kwana daya.


Macijiya za ta iya haihuwa sau biyu a shekara daya, wasu sukan haifi jariran macizai kai tsaye da ransu , yayin da wasu sukan haifi macizai ta hanyar sakin kwai, wanda yawansu zai iya kaiwa 150 a lokaci daya.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post