Kada ka zama kanwar-lasa a kan sha'anin 'Yan shi'a - JIBWIS ta shawarci Buhari


Legit Hausa

Kungiyar Jama'atu Izalitil Bid'ah Wa Ikamatis Sunnah JIBWIS, ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauka duk wasu matakai mafi dacewa wajen magance tarzomar da 'yan shi'a ke haddasawa a kasar nan. Kungiyar JIBWIS ta shawarci Buhari a kan kada ya sake ya zamto kanwar-lasa wajen daukar matakai da za su magance munanan hare-hare da zangar-zangar 'yan shi'a ke haifarwa wajen tayar da zaune tsaye a kan jami'an tsaro da kuma sauran al'ummar Najeriya wadanda ba su ji ba kuma ba su gani ba.

Shawarar JIBWIS na zuwa ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Yulin 2019, cikin wata sanarwa daga bakin jagoran ta, Sheikh Sani Yahaya Jingir, da ya gabatar yayin ganawa da manema labarai a ofishin sa dake birnin Jos na jihar Filato. Sheikh Jingir ya jaddada cewa, kasancewar su kungiyar musulmi, ba za su zuba idanu a kan yadda al'amura ke neman tabarbarewa cikin kasar nan ba tare da tofa albarkacin baki ba da kuma bayar da gudunmuwa gwargwadon iko.

Ya gargadi majalisar dattawa a kan kada ta kuskura tantance duk wanda ta samu da nasaba cikin jerin zababbun ministocin Buhari ta kusa ko nesa ko kuma alakar goyon bayan masu akidar shi'a da sauran kungiyoyi masu neman rabuwar kai a kasar nan. Cikin kalaminsa, "mun fahimci cewa cikin zababbun ministocin Buhari akwai mai goyon bayan akidar shi'ada ko kuma goyon bayan masu neman kawo rabuwar kai a kasar nan. Kada majalisar dattawa ta kuskura ta tabbatar da ire-iren su a matsayin jagorori a kasar nan."

 "Abin takaici ne a samu cewa akwai wadanda ke daukar makamai domin yakar 'yan sanda tare da yunkurin kai hari majalisar tarayyar Najeriya. Baya ga hakan su na ikirarin neman samun damar kashe 'ya'yan shugaban kasa Buhari ko kuma shi a karan kansa yayin da suka samu babbar dama." "Mu na fatan shugaban kasa Buhari ba zai ragawa wannan kungiya ba wajen daukar tsauraran matakai ta hanyar umartar hukumomin tsaro da su zage dantse wajen magance ta'addancin masu goyon bayan akidar shi'a."
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post