Allah mai iko: An wayi gari wani babban tafkin ruwa dake kasar Rasha ya rikide ya koma tafkin jini


Legit Hausa

Wani abu da ya faru mai cike da abin al'ajabi a wani kauye a kasar Rasha, yayin da mutanen kauyen suka wayi gari suka iske koramar da suke diban ruwa a cikinta ruwan cikin ya gurbace ya koma jini. Lamarin dai ya faru a kauyen mai suna Norilsk dake kasar ta Rasha a wata korama da mutanen kauyen ke kiranta da Daldikhan.

Mutanen kauyen sun bayyanawa manema labarai cewa, lafiya lau suka kwanta suka bar koramar, ma'ana ruwan lafiyarshi kalau a daren ranar da lamarin ya faru, amma kuma wayewar garin ke da wuya suka tarar da ruwan ya koma na jini. Kullum dai abubuwan ban al'ajabi kara faruwa suke a duniyar nan, kuma Allah ne kadai ya san dalilin da yasa yake bayyana abubuwan ga bayinsa.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post