• Labaran yau

  Tirkashi: Rashin sunan Ali Nuhu a cikin jerin Ministocin da Buhari ya fitar ya jawo kace - nace


  Legit Hausa


  A kwanakin baya an yi ta yada jita-jitar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai mika sunan fitaccen dan wasan Hausa na Kannywood Ali Nuhu Mohammed a matsayin Ministan matasa da wasanni. Sai dai kuma a sunayen shugaban kasar ya bayar domin a tantancewa su babu sunan Ali Nuhu a ciki.

  Wannan lamari ya janyo kace-nace a kafafen sada zumunta. Sardaunan Matasan Rijiyar Lemo dake jihar Kano cewa yayi: "Wai shi Ali Nuhu da ake cewa za a bashi kujerar Minista a karkashin wace jiha zai tashi? Kano, Gombe ko kuma Plataeu?" 

  Haka shi kuma wani shafin Hausa na Facebook mai suna Hausa7 sun sanya hoton Ali Nuhu ne yana fada da wani (kuma akwai yiwuwar an dauki wurin a cikin fim ne) amma sai suka ce daga majiya mai tushe sun jiyo cewa ya fara fada da abokanan aikinsa wanda yake tunanin sune suka yi masa kafar ungulu.

  Haka ita ma wata mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook mai suna Husnah Ahmad ta sanya hotunan gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da shugaban jam'iyyar jihar Kano na APC, Abdullahi Abbas da kuma Ali Nuhu, inda a karshe tayi wani rubutu na hirar barkwanci kamar haka:

  Ali Nuhu: Gwamna ban ji sunana ba cikin ministocin nan?

  Ganduje: To kai banda abinka nima ba a saka sunan wadanda na bayar ba.

  Ali Nuhu: Au dama baka sanya sunana ba kenan?

  Ganduje: Na manta ne.

  Audu Ciranci: To kai Ali Nuhu ai nima ba a saka sunana ba!

  Ali Nuhu: To ai kai bakada ilimi
   

  DAGA ISYAKU.COM

  Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

   Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tirkashi: Rashin sunan Ali Nuhu a cikin jerin Ministocin da Buhari ya fitar ya jawo kace - nace Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });