Dan jam'yar adawa da Buhari zai ba Minista ya koma jam'iyar APC


Legit Hausa

Yan sa’o’i kadan bayan sanar dashi a matsayin daya daga cikin zababbun ministocin shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan majalisar wakilai, Emeka Nwajiuba, ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar Accord Party zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Jawabin sauya shekar Nwajiuba na kunshe ne a cikin wata wasika da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wasu ya karanto a zauren majalisa. Dan majalisar na jihar Imo, wanda ya samu siga majalisar wakilai ta tara a karkashin inuwar jam’iyyar Accord Party, ya ci moriyar hukuncin kotu ne da ta tsige Chike Okafor na APC.

Kotu ta bayyana cewa jam'iyyar APC bata bi ka'idoji wajen zabar Okafor ba. kafin sauya shekarsa zuwa Accord, Nwajiuba, wanda ke wakiltan mazabar Ehime Mbano/Ihite Uboma/Obowo na jihar Imo, ya kasance dan APC. Kasancewarsa dan kashenin Buhari, bai zamo abun mamaki ba a lokacin da sunan Nwajiuba ya bayyana a cikin jerin sunayen ministoci 43 da aka gabatarwa majalisa duk da kasancewarsa dan jam;’iyyar adawa.

A wani labari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Godswill Akpabio wanda sunansa ke cikin jerin sunayen sabbin ministocin da Buhari ya aikawa majalisa, ya ce zai yi iya bakin kokarinsa a duk ma’aikatar da Shugaban kasa ya damka masa. Akpabio ya fadi wannan maganar ne yayin hirarsa da manema labarai jim kadan bayan majaliasar dattawa ta kammala tantance shi a ranar Laraba.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post