Babbar magana: Mataimakin gwamnan Kogi zai kai karar gwamnansa kotu


Legit Hausa

Simeon Achuba, mataimakin gwamnan jihar Kogi ya yi ikirarin cewa zai kai karar Gwamna Yahaya Bello zuwa kotu bisa rashin biyansa albashi tun na shekarar 2017, kudin da jimillarsu ta kama N819m. Achuba wanda ya kasance mataimakin gwamnan na Kogi tsawon shekaru biyu kenan yanzu, ya rubuta ma gwamnan wasika ta hanyar lauyansa Cif Femi Falana ( SAN).

A cikin wasikar ya nemi Gwamna Bello ya biya shi hakkinsa cikin mako guda kacal. A yau Laraba 24 ga watan Yulin 2019 ne wa’adin mako gudan da mataimakin gwamnan ya bada ke cika. Manema labarai na cigaba da zuba ido domin ganin abinda zai biyo bayan cikar wa’adin na mako guda. Idan baku manta ba, a kwanakin baya, ma’aikatan jihar Kogi sun bayyana bacin ransu sakamakon rashin biyansu albashin da gwamnan jahar bai yi.

Wannan al’amari yayi kamari kwarai da gaske saboda ba wai ma’aikata kadai suka koka da lamarin ba hadda masu karbar fansho. A cewar da dama daga cikinsu, “ Muna cikin tsaka mai wuya, mun rasa inda zamu sa kanmu.”

Haka zalika, lamarin rashin biyan albashin ya fusata Kungiyar Malamai ta kasa wato NUT, inda shugaban kungiyar reshen jihar Kogi, Thomas Ayodele ya ce, malaman makaranta ne ya kamata a ce sune kan gaba wurin karbar albashi amma sai gashi abin takaici anyi biris da al’amarinmu.

Wani malamin makarantar firamare, Audu Austin ya bamu labarin cewa, ana dadewa ba a biya albashin ba kuma idan ma an tashi biya ba cikakken albashin ake badawa ba.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post