Legit Hausa
Kotun da ke sauraron korafe korafe
kan zaben gwamnan jihar Kano ta amince da bukatar jam'iyyar PDP na binciken
kayayyakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi amfani da su
wajen gudanar da zaben gwamnan jihar.
Dan takarar gwamnan jihar karkashin
jam'iyyar PDP Alhaji Abba Kabiru Yusuf na kalubalantar nasarar da hukumar zaben
ta ce gwamna Abdullahi Ganduje na jam'iyyar APC ya samu a zaben gwamnan jihar
da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris.
A cikin wata takardar korafi da ya
gabatar gaban kotun, wacce ke karkashin mai shari'a Halima Shamaki, lauyan dan
takarar PDP, Maliki Kuliya-Umar ya bukacin kotun da ta umurci INEC ta baiwa
jam'iyyar kayayyakin da aka gudanar da zaben da su a ranar 9 ga watan Maris da
kuma 23 ga watan Maris domin ta yi bincike kan su.
Mai shari'a Shamaki ta umurci INEC
da ta baiwa jam'iyyar dukkanin kayayyakin zaben da ta yi amfani da su wajen
gudanar da zaben Kano, bisa ga dalilan da jam'iyyar ta bayar na son binciken
kayayyakin. Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa jam'iyyar
PDP na da kwanaki biyar ta shigar da APC kara kotu bayan da ta cinye kwanaki 15
cikin 21 da dokar zaben kasar ta 2010 ta tanar kamar yadda aka sabunta.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi