Gwamnatin jihar Kebbi bata saukar da Kwamishinoninta ba

Gwamnatin jihar Kebbi bata saukar da Kwamishinoninta ba kamar yadda ake yadawa a shafukan sada zumunta. Wannan ya biyo bayan jita jita da wasu ma'abuta amfani da kafofin sada zumunta ke yadawa a shafukansu yan kwanaki da suka gabata a jihar Kebbi.

Wata majiya kwakkwara ta shaida mana cewa ba haka zancen yake ba. Majiyarmu ta ce wata takarda ce Gwamnatin jihar Kebbi ta rubuta zuwa ga Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi inda ta bukaci ya aika takardun ga Kwamishinoni, kuma ana bukatar su rubuto wa Gwamnati rahotun ma'aikatarsu yadda lamaurra suka kasance daga 2015 zuwa 2019 tare da bayani inda ake da matsaloli a ma'aikatunsu da shawara yadda za'a magance su.

Wannan salon al'ada ce ga kowane zangon mulki a matakai na shugabanci matukar mulki ya zo karshe, kafin a saukar da zubin jerin shugabannin ma'aikatu.

Hakazalika idan har Gwamnati ta saukar da Kwamishinoni za ta bayar da sanarwar haka ta hannun Sakataren watsa labari na gidan Gwamnati watau CPS, ko ta ofishin Sakataren Gwamnatin jiha, ko ta hanyar kiran taron manema labarai.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN