Da duminsa: Rundunar soji ta yi arangama da mayakan Boko Haram kan hanyar Damaturu-Maiduguri


Legit Hausa

Rahotanni daga gidan talabijin na TVC na nuni da cewa a yanzu haka dakarun rundunar soji na musayar wuta da mayakan Boko Haram kan hanyar Damaturu-Maiduguri.

Rahotanni sun bayyana cewa mazauna yankin da ake musayar wutar sun shiga gidajensu tare da garkamewa domin gudun kisan wanda bai ji ba bai gani ba.

Haka zalika rahotanni sun bayyana cewa an ga jiragen yakin rundunar soji na sama da ke luguden wuta kan mayakan Boko Haram. Cikakken labarin yana zuwa...

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post