Legit Hausa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi
kira shuwagabannin duniya da su samar da hanyoyi da za’a zamanantar da mutanen
duniya da ababen qere-qere wadanda kowa zai iya mora cikin sauki da tsaro.
A cewar wani jawabi daga kakakin
shugaban kasa, Femi Adesina a Abuja, shugaban kasar ya bayyana kalubalen a
jawabin da yayi a taron zuba jari na shekarar 2019 a Dubai a ranar Litinin, 8
ga watan Afrilu.
Shugaban kasar yace akwai bukatar
killace martabar Tattalin arziki mai tafiya da fasahohin zamani. Taken taron
shine: “Mapping the Future of Foreign Direct Investment: Enriching World
Economies through Digital Globalisation.”
Yayinda yake jawabin cewa kayan
kimiyar zamani na duniya na kawo sauyi a duniyar kusan kullun, shugaban
Najeriyan ya yi gargadin cewa kimiyar zamani da ya game duniya zai ci gaba da
zama barazana idan aka barshi ba tare da kula ba.
Shugaban kasar ya koka kan yadda ake
amfani da kimiyar ta zamani wajen magudin zabe, karkatar da yancin
damokradiyyar al’umman kasa da kuma tayar da rikici.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi