Type Here to Get Search Results !

A dora laifin kashe-kashen Zamfara kan Ministan Tsaro, ba a kan Gwamna Yari ba - Kungiya


Legit Hausa

Wata kungiyar sa kai mai neman yancin al’umma, mai suna PAIR, ta dora alhakin munanan hare-haren da ake kai wa jihar Zamfara a kan Ministan tsaro, Mansur Dan Ali, maimakon a kan Gwamna Abdul’aziz Yari na jihar.

Baya ga PAIR kungyoyin SGE, NEO da TPC ma sun daura alhakin a kan ministan, kuma sun ce Dan-Ali bai yin wani gagarimin hobbasan da za a gani har a yaba cewa da gaske ya ke yi wajen ganin an magance fitinar.

Gamayyar Kungiyoyin sun ce Yari ya yi iyakar bakin kokarinsa da dokar kasa ta wajabta masa, ta hanyar bayar da taimakon kayan aiki, sadarwa da bayanai, bayar da gidaje da kuma alawus na musamman ga ‘yan sanda da sojojin da aka tura a Zamafara, ba tare da wani samun taimako daga Ma’aikatar Tsaro ba.

A cikin wata sanarwa da Isa Yaro ya sa wa hannu, a madadin Gamayyar Kungiyoyin, a jiya Lahadi a Abuja, ya nuna rashin jin dadin yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa shawo kan wannan fitina a Jihar Zamfara sama da shekara biyu.

Isa ya ce tun tuni ya kamata a ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kori Ministan Tsaro, Mansur Dan Ali. Yaro ya ce ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya yi karatun ta-natsu, ya san irin mutanen da zai nada kan mukamai idan an shiga sabon zangon mulki na biyu a ranar 29 Ga Mayu.

 DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN