Legit Hausa
Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya
shawarci gwamnatin tarayya da ta yi amfani da mafarauta domin magance matsalar
garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta'addanci da ke ci gaba da mamaye shiyyar
Arewacin Nigeria.
Sarki Sanusi, wanda ya bada wannan
shawarar a yayin wani taro na shuwagabannin mafarauta a Kano a ranar Lahadi
karkashin kungiyar masu kishin ci gaban jihar Kano (KCCI), ya ce jihar Kano ta
gwada irin hakan, kuma an samu nasara.
Da ya samu wakilcin hakimin Doguwa,
Dan Amar na Kano, Alhaji Aliyu Harazimi, Sanusi ya ce a cikin shekaru hudun da
suka gabata, Kano ta Kudu ta kasance cikin fargaba saboda yawaitar garkuwa da
mutane da kuma fashi da makami. Ya ce:
"A lokacin da garkuwa da mutane
ya tsananta a dajin Falgore da ke karamar hukumar Doguwa, mun gayyaci mafarauta
kuma muka samar da watatawagar tsaro ta musamman da suka hada da sojoji, 'yan
sanda, civil defence da maharba.
"Mun samu nasarar lalata
sansanonin masu garkuwa da mutane guda shida da ke a cikin dajin. A yanzu dai
shekaru hudu ke nan tunda jami'an suka kai wannan sumame, har yanzu bamu sake
jin an yi garkuwa da wani a dajin ba." Sarki Sanusi ya baiwa gwamnatin
tarayya shawara kan cewar ya kamata ta samar da makamanciyar wannan tawagar
domin kawo karshen garkuwa da mutane a jihohin Zamfara Kaduna da sauran jihohin
da lamarin ya shafa.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi