Yansanda sun tsayar da matukin wata mota kirar Porsche Panamera wacce aka yi ma penti ruwan zinare kuma suka bukaci ya sauka daga titi saboda motarsa tana kyalli da yawa, domin zai iya kawo hadari a kan titi ta hanyar kashe ma wasu matuka ababen hawa ido.
Shi dai wanda aka tsayar dan shekara 31, ya mika ma yansanda makullai da takardun motar shi ne bayan yansanda sun bukaci ya yi haka a birnin Hamburg da ke kasar Germany,Yansanda watau Jamus.
Daga bisani yansanda sun ja motarsa zuwa ofishinsu inda suka yanka masa tara kuma ya biya kafin aka bari ya dauki motarsa.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi