'Yan majalisa sun fito da sabbin hanyoyin yiwa masu satar mutane basaja


Legit Hausa

Cikin dabarun da suka bullo da ita shine dena amfani da lambar motoccinsu da ke nuna cewa su 'yan majalisun tarayya ne. Wadanda su kayi magana da majiyar Legit.ng sun ce 'yan majalisun sun dauki wannan matakan ne saboda suna tsoron masu garkuwa da mutane. Sun kuma ce 'yan majalisun sun dena sanar da mutane wuraren da za su tafi har hadimansu da masu aiki a gidajensu ma ba su amince da su ba a yanzu.

Sun ce wasu tsirarun amintattunsu ne kadai suke sanin inda za su tafi da lokutan tafiyarsu da dawowa. Ra'ayoyin 'yan majalisar ya rabu a kan batun tafiya tare da masu tsaron su a hirar da su kayi da Saturday Punch.

A makon da ta gabata, mun ruwaito muku cewa wasu daga cikin jiga-jigan 'yan Najeriya sun dena bin hanyar Abuja zuwa Kaduna saboda tsoron masu garkuwa da mutane. Hakan ya sa farashin tikitin jirgin kasa ya yi tashin gauron zabi saboda yanzu al'umma sun gwammace suyi tafiya a jirgin kasan.

Wani dan majalisa daga yankin Arewa maso Tsakiya ya ce yanzu a boye ya ke tafiya inda ya kara da cewa wadanda suke tare da shi ba su sanin inda ya ke tafiya a yawancin lokuta. Wani dan majalisar, Mr Olusegun Odebunmi ya ce baya tunanin amfani da lambar gwamnati a wajen Abuja abu ne mai kyau a yanzu saboda tsaro.

Ya ce: "Muna cikin hatsari. Idan kana zaune a cikin Abuja ne toh babu laifi idan kayi amfani da lambar gwamnati amma idan za ka fita daga Abuja zai fi kyau ka cire lambar sai dai idan kana tare da masu tsaronka na musamman."

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN