Wata gobara da ta tashi da daren ranar Juma'a ta yi sanadin konewar shaguna shida a babban kasuwar garin Birnin kebbi.
Wutar ta shafi sashen shagunan kayakin aikin noma kamar yadda Malam Aminu Shehu wani mai gadi a kasuwar ya shaida ma wakilin kamfanin jakadancin labarai na Najeriya NAN.
Shehu ya ce wutar ta tashi ne da misalin karfe 10 na daren Juma'a, kuma babu wanda ya san musabbabin tashin wannan gobara kawo yanzu.
Sashen kashe gobara na jihar Kebbi ta yi kokari wajen dakile wutar daga ci gaba da bazuwa.
Sai dai hukumar kashe gobara na jihar Kebbi da yansanda basu ce komai ba dangane da lamarin kawo yanzu.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi