Legit Hausa
Gwamnan jihar Osun ya bukaci
hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya da su sanya ido akan 'yan ta'addar jihar
Zamfara, wadanda yanzu ake tunanin sun fara canja sheka daga jihar Zamfara suna
shiga wasu jihohin A ranar Alhamis dinnan ne da ta gabata, gwamnan jihar Osun,
Adegboyega Oyetola, ya bukaci jami'an tsaro da sarakunan gargajiya da su lura
sannan kuma su dakile duk wani shiri na 'yan ta'addar jihar Zamfara, wadanda
suke yin kaura daga jihar suna komawa wasu jihohi.
Hakan ya biyo bayan sanarwar da
babban sakatarensa a fannin sadarwa ya fitar, Mista Adeniyi Adesina, bayan
gwamnan ya yi magana a wurin wani taro, akan gudanar da tsarin tsaro, wanda
sarakunan gargajiya, shugabannin hukumomin tsaro, kungiyoyin jama'a, 'yan siyasa,
'yan kasuwa da sauransu suka hallata a Osogbo. Oyetola ya ce "ya zama
wajibi a sanya matakan da za su magance matsalar 'yan ta'adda da ke faruwa a
jihar Zamfara shigowa jihar Osun."
Gwamnan ya jaddada bukatar tabbatar
da tsaro ta hanyar tattara bayanai, sannan sarakunan gargajiya su saka ido a
yankunansu da kuma bukatar a fadakar da jami'an tsaro su sanya ido wurin dakile
duk wani shiri na ta'addanci a jihar.
Gwamnan da kuma jami'an tsaro sun
gargadi masu bada gidajen haya, akan bai wa mutane wadanda ba su da kyakkyawar
masaniya a kansu. "Idan ka bawa mutumin da baka san shi ba hayar gida,
kuma muka gano cewa dan ta'adda ne, to duk abinda ya biyo baya kai ka jawowa
kan ka," in ji Oyetola.
Ya bukaci sarakunan gargajiya da su
yi aiki tukuru, domin masu hakar ma'adanai suna nan suna yawo a wasu yankuna na
cikin jihar." Gwamnatin tarayya ta hana hakar ma'adanai a jihar Zamfara,
bayan ta samu bayanan cewa 'yan ta'addar jihar su na da alaka da masu hakar
ma'adanai wadanda ba su da lasisi.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi