An sanya wa biri kwakwalwar mutum


Legit Hausa

Har ya zuwa yanzu birai ba su kwace duniyar nan ba. A karon farko, masana a fannin kimiyya sun sanya kwayoyin kwakwalwar dan adam a cikin birai.

Masu binciken na kasar China sun yi amfani da kwakwalwar biri don daukar kwayoyin hallittun MCPH1, abin da suka yi imani da shi shine yana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa kwakwalwar dan Adam.

Masanan sunce biri ya fi dacewa wurin yin gwajin basira kuma ya fi sauri fiye da biran da suke daji, sannan kuma kwakwalwarsu ta fi daukar lokaci wajen bunkasa, kamar kwakwalwar mutum. Amma kuma duk da haka, kwakwalwarsu ba ta kara girma. Birai biyar ne suka haye bayan an kammala gwajin.

Amma masu bincike sun ce gwajin bai saba wa dokokin kimiyya ba saboda kwayoyin halittan birai jinsin Macaque sun bambanta sosai da na mutane. Da yawa ba su gamsu ba. RSPCA, wata kungiyar kula da hakkin dabbobi da ke kasar Birtaniya ta ce, "Birai dabbobi ne da suke jin zafi da damuwa.

Kuma su na amfani da su wajen gwaje-gwajen da suka shafi dan Adam." An gudanar da binciken ne don gano yadda kwakwalwar dan Adam ke kara girma da bunkasa idan aka kwatanta da birai, wadanda suke da kashi 98 na kwayoyin halittun dan Adam.

Don haka masana kimiiyya suna so su gano wadanne kwayoyin halittu ne za su kara mana hazaka.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN