• Labaran yau

  Yadda yan daba suka yi ma wasu soji duka suka raunata su har da barnata motar soji

  Rahotanni daga jihar Lagos na nuna cewa wasu yan daba sun barnata wata motar soji kuma suka yi wa sojoji dan karen duka, tare da raunata su, sakamakon mutuwar wani saurayi mai suna Kola Mutiu wanda aka fi sani da suna Black Jesus ranar Talata.

  Majiyar isyaku.com ta ce Kola ya bi wata babbar mota ce kuma yana neman direban motar ya sallame shi, amma direban bai tsaya ba shi kuma Kola ya bishi a guje, ana cikin haka ne sai wata mota ta buge Kola aka garzaya zuwa Asibiti da shi.

  Ganin haka ke da wuya sai sauran yan daba suka afka wa direban babban motar da duka, yayin da haka ke faruwa sai ga sojoji a cikin motarsu suna wucewa, ganin haka ya sa suka tsaya domin su hana yan daban ci gaba da dukan direban babban motar.

  Daga bisani sai yan daban suka sami labari cewa ai Kola ya mutu a Asibiti. Nan ne fa lamari ya hargitse, domin dai yan daba sun yi kukan kura suka afka ma sojin su da kansu kuma suka yi masu raunuka, hakazalika yan daban sun barnata motar sojin.

  Saidai wata majiya ta shaida mana cewa, abin da yan daban suka aikata a kan sojin babban laifi ne kuma bai kamata su barnata dukiyar gwamnati ba tare da raunata jami'an soji.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda yan daba suka yi ma wasu soji duka suka raunata su har da barnata motar soji Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });