Barayi sun sace bindigogin yansanda tare da albarusai daga wani caji ofis na yansanda a Nandi da ke kasar Kenya ranar Talata bayan sun kula cewa yansanda da ke ofishin sun je kallon wasan kwallon kafa da aka buga tsakanin kungiyar kwallon kafa na Manchester United da Barcelona wanda aka buga da misalin karfe 9:30 na dare.
Majiyar isyaku.com ya ce hafsoshin sun dawo wajen aiki ne yan mintoci bayan tsakiyar dare, suka tarar cewa an balle kofofin caji ofis tare da kofar dakin da ake ajiye makamai.
Jami'in dansanda kofur Rodgers Masiwa ya shigar da kara a ofishin yasanda na Kobujoj, inda ya ce barayi sun sace makamai da suka hada da bindigogin yansanda kirar G3 FMP 77095029, G3 FMP 7709443 da G3 A3 F91879 tare da Magazine na albarushi mai girman 7.62mm har da wasu harsasai 17 da guda 20 a ofishin yansanda na Nandi na yamma.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi