A karon farko tun kafuwar Najeriya, an samu 'sa hannun' mace a kan takardar Naira


Legit Hausa

A karo na farko a tarihin Najeriya na shekaru 59 da wanzu wa, an samu 'sa hannun' mace, Priscilla Ekwere Eleje, a kan takardar Naira. Hakan ya biyo bayan tabbatar da Eleje, mukaddashiyyar babban darektan kudi da gudanar wa a babban bankin kasa (CBN), a matsayin darekta.

Eleje, ita ce mace ta farko a tarinhin CBN, da ta taba rike mukamin, sannan mace ta farko da taba 'sa hannu' a kan takardar Naira. Ladi Kwali, wata mata da ta kware wajen kera tukwanen tabo, ita ce mace ta farko da aka taba saka hotonta a jikin takardar Naira 20 (N20).

'Yan cikin gida a CBN, sun shaida wa majiyar Legit.ng cewar gwamnan CBN, Godwin Emefieke, ya na kokari matuka wajen tabbatar da cewar mata sun samu wakilci a cikin babban bankin, musamman a manyan mukamai.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post