Yadda aka kashe yara 6 diyan mutum 1 sakamakon rikicin kabilanci

Ranar Asabar da ta gabata, an kashe kuma aka kone gawakin wani mutum tare da iyalinsa bayan ya kai yayansa guda shida domin rubuta jarabawar share fage domin shiga Jami'a watar Matriculation a Jami'ar jihar Ebonyi (EBSU).

Rahotanni sun ce shida daga cikin yaran diyan mutum daya ne yayin da sauran aka kashe su ta hanyar harbi da bindiga.

An kai masu wannan hari ne  a Ndufu Alike kan titin Alex Ekweme, kusa da bakin iyakar al'ummar guda biyu da suka shefe shekara da shekaru suna fada tare da gaba da junansu a kan rikicin mallakar iyakar filayen al'umman guda biyu.

Kakakin yansandan jihar Ebonyi Loveth Odah ta ce lamarin ya faru ne ranar Asabar.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post