Legit Hausa
Rundunar 'yan sanda a jihar Kuros
Riba ta tabbatar da mutuwar wani jami'inta mai mukamin kwansatabul da wasu
tsageru suka kashe a ofishin hukumar zabe ta kasa (INEC) da ke karamar hukumar
Bakassi.
Da ta ke tabbatar da kisan jami'in,
DSP Irene Ugbo, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ya ce an kashe dan sandan
ne yayin da ya ke bakin aikinsa. Wasu tsageru ne suka kawo farmaki ofishin na
INEC tare da kashe jami'in dan sandan da ke aiki a wurin, kamar yadda Irene ta
fada.
Tayi watsi da zargin cewar kisan na
da alaka da zabukan shekarar 2019 da aka kammala. "A'a, ko kadan kisan dan
sandan bashi da wata alaka da INEC," kamar yadda ta fada.
Ta bayyana cewar tuni rundunar 'yan
sanda ta fara binciken kisan jami'in da aka yi ranar Litinin. Sai dai rundunar
'yan sandan ba ta bayyana sunan jami'in da aka kashe ba.
Wasu shiadar gani da ido sun bayyana
wa manema labarai a garin Calabar cewar dan sandan ya mutu ne sakamakon rashin
samun taimakon gaggawa yayin da jini ke zuba daga jikinsa sakamakon harbin da
aka yi masa.
Wani bincike da aka gudanar a
tsakanin mazauna Bakassi ya nuna cewar har yanzu tsagerun yankin na cigaba da
cin karensu babu babbaka, duk da yafiyar da gwamnatin jiha da ta tarayya tayi
masu bayan sun fito sun shaida tare da nuna wa duniya cewar sun ajiye makamansu.
Tsagerun yankin Bakassi na tsula tsiyarsu ne
karkashin wata kungiya 'Bakassi Strike Force' da wani mai suna Benjamin Ene,
wanda aka fi kira da 'Janar Franklyn, ke jagoranta.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi