Ya kashe matarsa da adda domin ta ce zata sake yin aure idan ya mutu

Wani bawan Allah mai suna Danjuma Bisalla ya fada hannnun yansanda bayan ya kashe matarsa Uwani domin ta ce za ta sake yin aure idan ya mutu.

Yansanda sun ce Bisalla ya amsa laifinsa cewa shi ya kashe Uwani, domin a lokacin da baya da lafiya ne ta yi furucin cewa idan ya mutu, ita za ta sake yin aure, sakamakon haka ya fusata ya dauko adda ya kai mata farmaki a lokacin da take barci a gidansu da ke kauyen Uddu karkashin Rijau a jihar Niger.

Bisalla ya ce "  Na yi mamakin jin matata tana gayamini a fuskana cewa idan na mutu sakamakon rashin lafiyata zata sake yin aure. Rayuwata ta bace matuka, sakamakon haka na yi mata rauni da adda a wuyanta wanda hakan ya zama ajalinta. Na kasheta domin kada ta sake yin wani auren tunda tana son in mutu.Bai kamata ta gaya mani wadannan kalamai ba a kunne na, wadannann kalamai suna da nauyi, shi ya sa na kasheta kuma Allah zai jefata a wutan Jahannama sakamakon wadannan mugayen kalaamai nata".

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN