Legit Hausa
Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen
jihar Kano, ta samu nasarar cafke wasu muggan makamai a ofisoshin jam'iyyar APC
da kuma na PDP da ke karkashin karamar hukumar Tudun Wada kamar yadda rahotanni
suka ruwaito.
Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito
cewa, hukumar 'yan sandan ta kuma samu nasarar cafke 'yan bangar siyasa takwas
masu alaka da wannan muggan makamai kamar yadda kakakin 'yan sandan jihar ya
bayyana, DSP Haruna Abdullahi.
Da ya ke bayar da tabbacin sa a kan
wannan lamari, DSP Abdullahi ya ce muggan makamai da suka shiga hannu sun hadar
da adduna, wukake, miyagun kwayoyi da kuma sauran muggan makamai masu barazana
ga lafiya.
Yayin tuntubar shugaban jam'yyar APC
na jihar Kano Abdullahi Abbas, ya shaidawa manema labarai cewa ba bu dan
jam'iyyar APC ko guda da ya shiga hannun jami'an tsaro a sanadiyar alakar sa da
makaman da ta kai hannu gare su. Cikin zayyana nasa jawabin, sakataren
jam'iyyar PDP na jihar Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya ce hukumar 'yan sanda ta
bayar da belin 'ya'yan jam'iyyar su bayan da ta gaza kama su da zargin da ta ke
tuhumar su.
Kazalika kwamshinan 'yan sandan
jihar CP Muhammad Wakil ya bayyana cewa, ya na nan daram kan bakin aikin sa
kuma an daina jin duriyar sa a halin yanzu sakamakon shudewar kakar zabe kamar
yadda ya bayyana manema labarai na BBC Hausa a makon da ya gabata.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi