Ala tilas Majalisar wakilai ta dage zamanta bayan yan Shi'a sun yi mata shigar bazata

Wasu mabiya mazhabar Shi'a karkashin Islamic Movement in Nigeria watau IMN sun shiga harabar Majalisar wakilai na Najeriya yanayi da ya sa ala tilasa Majalisa ta dage zamanta na yau .

Rahotanni sun ce yan Shi'an sun rinjayi yansanda a wannan lokaci kafin suka tilasta kansu suka shiga kofar farko na Majalisa.

A daidai wannan lokaci ne yanayi ya canja, domin gaba daya wajen ya dauki kabbara yayin da yan kungiyar suka dinga fadin "Allahu akbar" !!!.

Daga na kuma sai suka mike zuwa kofa ta biyu, amma a wannan mataki shugabanninsu sun roke su cewa kada su wuce gaba, hatta yansanda da aka ce sun tsere da farko sun bayyana a wannan mataki inda su ma suka shiga sahun bayar da hakuri ga yan kungiyar cewa kada su wuce gaba.

Masu zanga zangan suna bukatar a saki shugabansu Sheikh El-zakzaky wanda Gwamnati ta tsare shi tun 2015 a hannun hukumar DSS.

Yayin tunawa da ranar haihuwar Zakzaky bayan ya cika shekara 68, yan kungiyar sun ce za su canja salon zanga zanga da suke yi domin neman a sako shugabansu.

A baya dai wata Kotu ta bayar da belin Zakzaky, amma Gwamnati bata sake shi ba bisa abin da ta kira "dalilan tsaro".

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN