Type Here to Get Search Results !

Wata mata ta hada baki da danta, sun kashe mijinta


Legit Hausa


Hukumar 'yan sandan jihar Neja ta kama wata mata Hafsat Aliyu mai shekaru 50 a duniya, da danta Babangida Usman, da zargin hada baki suka kashe mahaifin yaron mai suna Ali Haruna. Lamarin ya faru ranar 13 ga watan Afrilu, 2019, a bayan makarantar firemare ta Shango dake karamar hukumar Chanchaga.

Rahotanni sun nuna cewa Usman da mahafiyarsa sun tarar wa mahaifin Usman din a lokacin da suka samu hatsaniya da mahaifiyar ta shi, inda ya lura da cewa mahaifin nasa ya na takurawa mahaifiyar ta sa a lokuta da dama.

A cewarsa, shi kawai ya yi kokarin ya kare mahaifiyarsa ne daga dukan da mahaifinsan ya ke mataa, inda shi kuma ya fadi ya mutu. Jami'in hulda da jama'a na hukumarr 'yan sandan jihar, Mohammed Abubakar, shine ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewar wadanda ake tuhumar sun amsa laifinsu.

Abubakar ya ce Usman da Mahaifiyarsa sun yiwa marigayin mummunan rauni, wanda ya mutu yayin da aka kai shi asibitin Ibrahim Badamasi Babangida don yi mishi magani, ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan sun kammala bincike.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN