Abba Kabir Yusuf shi ne ainihin ‘Dan takarar PDP a Kano inji Kotu


Legit Hausa

Mun samu labari cewa Babban kotun daukaka kara da ke zama a Garin Kaduna ta tabbatar da takarar Injiniya Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar PDP mai adawa a jihar Kano a zaben da ya gabata na 2019.

Kotu tace babu shakka Injiniya Abba Kabiru Yusuf shi ne tabataccen ‘dan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Kano na bana. Kotun ta rushe hukuncin da wani Alkalin babban kotun tarayya da ke zama a Kano yayi kwanakin baya.

Alkali mai shari’a Tanko Hussaini na kotun daukaka karar da ke Kaduna ya bayyana cewa tun farko kotun tarayya da ke Kano tayi kuskure da tayi watsi da takarar Abba Yusuf bayan karar da wani Ibrahim Little ya shigar gaban ta.

Babban Alkalin kotu yake cewa Alhaji Ibrahim Little bai da hurumin da zai kalubalanci matakin da jam’iyyarsa ta dauka. Haka kuma Alkalin ya bayyana cewa Alhaji Little bai cikia sharudan da su ka dace wajen shigar da kararsa ba.

Wannan ya sa mai shari’a Tanko Hussaini ya tabbatar da takarar Abba Yusuf a PDP yana mai raba gardamar rikicin da wasu ‘yan jam’iyyar adawar su ke yi, inda su kace ba su yarda cewa shi ne ainihin mai rike da tutar jam’iyya ba.

A baya wani Alkali, yace ba ayi zaben fitar da gwani a PDP ta jihar Kano ba. Jam’iyyar ta musanya wannan inda tace Abba Yusuf ne ya zo na 1 a zaben fitar da gwaninta, sannan Jafar Bello, Sadiq Wali da Salihu Takai su ka biyo baya.

 DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN