Legit Hausa
Uwargidan shugaban kasa, Hajiya
Aisha Buhari ta bayyana kudurinta na bude jami’a mai zaman kanta wacce zata
sanyama suna “Jami’ar Muhammadu Buhari”.
Tayi wannan furucin ne ranar Assabar
wurin wani taro da ta hada a Yola tare da masu kishin garin na Adamawa. Aisha,
wacce bata fadi lokaci ko wurin da wannan jami’ar zata kasance ba, tace za’a
bude wannan jami’ane ta hanyar hadaka da kasashen Sudan da Qatar.
Da take zayyana matsalolin dake
fuskantar ilimi a jihar da ma sauran sassa daban-daban na jihar, Aisha tayi
kira ga yan asalin wannan jiha ta Adamawa da suyi iya bakin kokarinsu domin
marawa gwamnati baya wajen shawo kan matsalar.
“Ba zan iya cewa ga abinda zamuyi ba na tilas
domin bada taimakonmu ga kokarin da gwamnati keyi ba, sai dai kawai zan iya
bada shawarwari akan irin ababen da idan mukayi zasu taimaka kwarai da gaske.
“A daidai wannan gaba, zan so a bude
wani asusu na musamman a jihar Adamawa wanda zai kasance ya ta’allakane fannin
ababen kawo cigaba a fadin jihar nan, ta yanda za’ayi amfani da kudin kana kuwa
a kaddamar da ayukan.”
Ambasada Fati Ballah ita kuwa kira
tayi ga al’ummar jihar, da su kasance masu hakuri da juna sa’anan kuma ta bada
shawarar cewa yakamata a kafa kwamiti wanda zai kawo tsare-tsaren da za’a bi
domin ciyar da jihar tasu gaba.
Manya-manyan mutane da dama sun
halarci wannan taro daga cikinsu akwai; Alhaji Sadiq Daware, Farfesa Shehu Iya,
Farfesa Auwal Abubakar, Mrs Hellen Mathias, Mallam Umar Abubakar, Janar Buba
Marwa da wasu jiga-jigan jam’iyun APC, PDP da ADC.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI