Komai ya kammala a zancen auren Jarumi Adam Zango a karo na shida

Legit Hausa Adam A. Zango, jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, ya kammala shiti tsaf domin angonce wa ...


Legit Hausa

Adam A. Zango, jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, ya kammala shiti tsaf domin angonce wa a karo na shida cikin shekara 13. A katin gayyatar daurin auren da majiyar mu ta gani da idonta, Zango zai angonce da wata mai suna Safiya Umar Chalawa, wacce aka fi kira da Suffy, a ranar juma'a mai zuwa da misalin karfe 2:30 na rana.

Za a daura auren ne a masallacin fadar sarkin Gwandu da ke garin Gwandu, a jihar Kebbi. Majiyar mu ta sanar da mu cewar Zango ya yi aure sau biyar a baya, ya samu 'ya'ya shida; hudu maza, biyu mata, daga mata biyar da ya aura kafin su rabu. Amina ce matar Zango ta farko da ya aura a shekarar 2006.

Ita ce uwar yaron sa na farko, Haidar, wanda yanzu haka ya cika shekara 12 da haihuwa. Majiyar mu ta ce ba ta san abinda ya raba auren Zango da Amina ba. Zango ya kara auren wata matar mai suna A'isha, 'yar asalin Shika ta karamar hukumar Zaria a jihar Kaduna.

Ta haifa masa 'ya'ya maza uku. Jarumin ya auri matar sa ta uku mai suna Maryam daga jihar Nasarawa. Daga bisani ya auri wata jarumar fim mai suna Maryam AB Yola a Lugbe, Abuja a shekarar 2013. Sun bayyana tare a cikin wani shirin fim din Hausa mai suna 'Nas' A shekarar 2015, Zango ya auri Ummul Kulsum daga Ngaoundere a jamhuriyar Kamaru.

An yi auren a sirrance. Ummul Kulsum ce ta fara haifa wa Zango diya mace, wacce ya sanya wa suna Murjanatu. Safiyya ko kuma Suffy kamar yadda ake kiranta, ita ce za ta kasance matar Zango ta shida da ya aura. Majiyar mu ta ce Zango ya saki dukkan mata biyar da ya aura a baya, sai dai har yanzu ba ta san dalilin rabuwar sa da matan da ya ke aura ba.

 DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
IDAN KA GAN WANI ABU NA FARUWA, HANZARTAB KA SANAR DA MU A ISYAKULABARI@GMAIL.COM
Name

'YANSANDA,1,AL-AJABI,22,AREWA,45,BIDIYO,147,BINCIKE,1,BIRNIN-KEBBI,375,BOLLYWOOD,2,BUHARI,10,DUNIYA,109,ENGLISH,25,FADAKARWA,126,FASAHA,14,FITACCEN LABARI,19,HOTO,175,HOTUNA,90,JAKAR MAGORI,1,LABARI,2977,NISHADI,282,OSCAR,2,Samaila Yombe,42,SANARWA,31,SHARHI,16,SIYASA,387,TARIHI,11,TSARO,353,WASANNI,18,
ltr
item
ISYAKU.COM: Komai ya kammala a zancen auren Jarumi Adam Zango a karo na shida
Komai ya kammala a zancen auren Jarumi Adam Zango a karo na shida
https://2.bp.blogspot.com/-U0qvC7U3LGc/XLyUchol-yI/AAAAAAAAVko/AtTnjc7ny98P0PUPNGI5vDA6HNny-8SjQCLcBGAs/s1600/zango.jpg
https://2.bp.blogspot.com/-U0qvC7U3LGc/XLyUchol-yI/AAAAAAAAVko/AtTnjc7ny98P0PUPNGI5vDA6HNny-8SjQCLcBGAs/s72-c/zango.jpg
ISYAKU.COM
https://www.isyaku.com/2019/04/komai-ya-kammala-zancen-auren-jarumi.html
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/2019/04/komai-ya-kammala-zancen-auren-jarumi.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy