Legit Hausa
Kotu ta yi watsi da zaben Sanata
Ademola Adeleke a matsayin dan takarar jam'iyyar PDP, a zaben gwamnan jihar
Osun da aka gudanar a Satumbar 2018
Kotun ta ce Adeleke ya karya dokar
sashe na 177 da ke a kundin dokar kasar da ya ce wajibi ne dan takarar gwamna
ya mallaki matakin karatu har zuwa sakandire
Sai dai lauyan Adeleke ya
kalubalanci wannan hukunci da mai shari'a Musa ya yanke, yana mai cewa zai
daukaka kara Mai shari'a Oathman Musa a wata babbar kotu da ke da zama a
karamar hukumar Bwari a Abuja a ranar Talata ta yi watsi da zaben Sanata
Ademola Adeleke a matsayin dan takarar jam'iyyar PDP, a zaben gwamnan jihar
Osun da aka gudanar a watan Satumba 2018.
Adeleke, wanda ke wakiltar mazabar
Osun ta Yamma a majalisar dattijai, shi ne ya lashe tikitin tsayawa takarar
gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar
a watan Satumba.
Wasu kusoshin jam'iyyar APC guda
biyu, Wahab Raheem da Adam Habeeb, a shekarar 2018, kwanaki kadan da zaben
gwamnan jihar Osun, sun maka Adeleke gaban kotu, inda suka zarge shi da gaza
mallakar sahihan takardun makarantar kammala sakandire, wanda a cewarsu bai
cancanta ya tsaya takarar gwamnan jihar ba.
Da ya ke yanke hukunci a ranar
Talata, mai shari'a Musa, ya soke zaben Adeleke a matsayin dan takarar PDP
kasancewar ya karya dokar sashe na 177 da ke a cikin kundin dokar kasar na 1999
da aka yiwa kwaskwarima.
Sashen ya ce wajibi ne dan takarar
kujerar gwamna ya mallaki matakin karatu har zuwa sakandire. A cewar mai
shari'a Musa, a yayin da kotun ta tattara bayanai kan cewa Adeleke ya shiga
makarantar sakandire a shekarar 1976, babu wani bayani da ya nunacewa ya
kammala karatun kasancewar babu sunansa a cikin kundin daliban makarantar tun
daga 1980.
Mai shari'a Musa ya kara da cewa
takardar kammala makarantar da ke cikin kundinsa na CF001 wanda ya gabatarwa
INEC na jabu ne, saboda an samu bayanai da suka banbanta kamar yadda shugaban
makarantar Ede Muslim, Ede, jihar Osun ya gabatar.
A wani labarin makamancin wannan,
lauyan Adeleke, Nathaniel Oke SAN ya kalubalanci wannan hukunci da mai shari'a
Musa ya yanke, yana mai cewa mai shari'ar ya fita daga hurumi ta yadda har ya
samo wasu hujjoji marasa tushe da ya yanke hukuncin da babu adalci a ciki.
Ya jaddada cewa kotun ta yi biris a
lokacin da aka gabatar mata da takardun WAEC na shaidar cewa Adeleke ya yi
karatu har zuwa makarantar sakandire.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi