Type Here to Get Search Results !

Zababen gwamnan jihar Zamfara ya shigar da karar INEC a kan takardan cin zabe


Legit Hausa

A kalla jam'iyyun siyasa 20 ne daga jihar Zamfara su kayi karar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC a kan rashin bawa zababen gwamnan jihar Zamfara da 'yan majalisun dokokin jihar takardun shaidan cin zabe.

Ebenezer Adabaki ne ya shigar da karar a ranar Talata a babban kotu da ke zamanta a Abuja a madadin masu shigar da karar. Wadanda suka shigar da karar sun hada da Shugaban kungiyar jam'iyyun siyasa na Zamfara, Zayyanu Haske, Zababen gwamnan jihar, Mukhtar Idris, mataimakinsa, da zababun 'yan majalisun dokoki 24.

Masu shigar da karar suna son kotu ta tabbatar idan sashi na 133(1) da 155 na dokar zabe ya bawa INEC ikon hana ko rashin bayar da kula ga batun bawa 'yan takarar da suka ci lashe takardun shedan cin zaben.

"Shin ko matakin da INEC ta dauka na dakatar da bayar da takardan shaidan cin zabe ga 'yan takarar da suka lashe zaben gwamna da 'yan majalisun tarayya na jihar Zamfara bai sabawa doka ba ko kuma sakacin aiki.

" Wadanda suka shigar da karar sun bukaci kotu ta tursasawa INEC bawa zababen gwamnan da mataimakinsa da sauran mambobin majalisar dokokin jihar ba tare da bata lokaci ba. Sai dai a halin yanzu ba tsayar da ranar da za a fara sauraron shari'ar.

DAGA ISYAKU.COM

 Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN