Rikicin Kaduna: Karanta abin da shugaban CAN ya gaya wa Kiristochi


Legit Hausa

Hadaddiyar kungiyar kiristocin Najeriya tayi kira ga ilahirin kiristocin dake karamar hukumar Kajuru dasu daina jiran dakarun Sojin Najeriya ko kuma Yansanda da nufin su karesu, su dauki makamai su fara kare kansu kawai.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kungiyar CAN, Joseph Hayab ne ya bayyana haka yayin da yake mika kayan tallafi da uwar kungiyar CAN ta kasa ta baiwa mutanen da rikicin kabilanci dana addini ya shafa a yankin.

“Ina kira ga yan uwana kiristoci damu daina jiran gwamnati ta kare yankunanmu, muma zamu iya kare kanmu, idan har zaka iya gina gidan kanka, amma kuma kana jiran Sojoji ko Yansanda su kareka toh kana da matsala.

“Babu wata doka a Najeriya data hanaka kare kanka, ita kawai doka ta hanaka cutar da wani ne, don haka bamuce ku cutar da wani ba, amma ku kare kanku, kare gidanka nada goyon baya a kundin dokokin kasa.”

Inji shi. Sai dai a wani mataki na mi’ara koma baya kuma, Faston yayi kira ga gwamnati data kare al’ummomin da makiyaya suka lahantasu domin su samu damar komawa gona duba da cewa damuna na karatowa, inda ya bada tabbacin CAN zata basu abincin ci, kuma zata basu kayan gini don sake gidajensu.

 DAGA ISYAKU.COM 

 Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews 

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM 

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN