Legit Hausa
Kananan yara yan kasa da shekara 2
da haihuwa bai kamata ace ana barinsu gaban talabijin ba, Wannan wata sabuwar
ka’idane da ta fito daga bakin kungiyar lafiya ta duniya.
Abinda yafi da cewa da yaran suyi
shine karatu ko kuma mai lura da su ya basu labari, ko da na awa guda ne.
Har wa yau, yara masu shekara 2 zuwa
4 zasu iya yin kallon na awa daya kacal shima din ba a ko da yaushe ba. Ku bar
barin kananan yara da jarirrai a gaban talabijin, shawara daga kungiyar lafiya
ta duniya (WHO) Bugu da kari, zama na tsawon lokaci gaban talabijin kan iya
haifarwa wadannan yara da rashin lafiya.
Yawan zaman da yara keyi gaban
talabijin kan haifar da matsalar kiba da ya wuce kima a turance ‘Obesity’. “
Yarinta wani lokacine da yaro kan iya daukan duk abinda ya taso a kai a
matsayin dabi’a wacce zata iya bin shi har girmanshi”.
A fadar shugaban kungiyar lafiya ta
duniya Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus. Domin haka abu mafi kyau shine a gina
yaran kan hanyar da zata inganta lafiyarsu ba wacce zata zame masu matsala ba.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi