Ni dan fashi da makami ne kawai, bana garkuwa da mutane

Legit Hausa Ba ainihin hoton dan fashin bane A jiya Alhamis ne 25 ga watan Afrilu, 2019, rundunar 'yan sandan jihar Neja ta ...


Legit Hausa

Ba ainihin hoton dan fashin bane
A jiya Alhamis ne 25 ga watan Afrilu, 2019, rundunar 'yan sandan jihar Neja ta ce ta kama mutane uku da yunkurin sace wani mutumi mai suna Chinedu Odenigbo da ke Angwan Kadara yankin Maitumbi, cikin garin Minna, babban birnin jihar Neja.

An shaidawa hukumar 'yan sanda faruwar lamarin ranar 18 ga watan Afrilu, 2019, wanda wani mutumi mai suna Emenike Odenigbo ya kira hukumar ya ke bayyana mata cewa ya kama wasu mutane biyu suna kokarin sace mishi dan shi mai suna Chinedu.

Wadanda ake zargin, Onwan Onyedika mai shekaru 20 da Eze Athanasius mai shekaru 27 duka daga jihar Enugu, 'yan sandan da ke yankin Maitumbi ne suka kama su. Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin dalibi ne a jami'ar Najeriya, Nsukka, ya shiga harkar sace mutanen ne saboda ya samu ya yi kudi da wuri.

Dalibin mai suna Onyedika, wanda ke aji hudu a jami'a, ya bayyanawa manema labarai cewa abokinshi Sunday ne ya yaudare shi ya shigo da shi cikin wannan badakalar. Ya ce, "Sunday ya gaya mini cewa zai fara sana'a, kuma ya roke ni da in tafi tare dashi zuwa gidan dan uwanshi dake garin Minna domin muyi mishi fashi, inda ya ce yiwa dan uwan nashi fashi ita ce hanya daya kawai da zasu samu kudin yin sana'ar, sai ni kuma na bishi. "

Ban san yadda aka yi na tsinci kai na a cikin wannan matsalar ba. Ban san cewa abokin nawa na da wata manufa a ranshi ba. Gaskiyar magana na biyo shi ne don mu saci kudin 'ya'yanshi ba da niyyar zuwa mu saci danshi ba.

"Na ci amanar mahaifina wanda ya rasu, ba ni da wani dalili na shiga cikin wannan rikicin. Ban san yadda zan kalli mahaifiyata ba. Na ba ta rayuwata gaba daya." Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Muhammad Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa za a mika wadanda ake zargin zuwa kotu bayan sun kammala bincike a kansu.

DAGA ISYAKU.COM 

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM 

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
IDAN KA GAN WANI ABU NA FARUWA, HANZARTAB KA SANAR DA MU A ISYAKULABARI@GMAIL.COM
Name

'YANSANDA,1,AL-AJABI,22,AREWA,45,BIDIYO,147,BINCIKE,1,BIRNIN-KEBBI,375,BOLLYWOOD,2,BUHARI,10,DUNIYA,110,ENGLISH,27,FADAKARWA,126,FASAHA,14,FITACCEN LABARI,19,HOTO,175,HOTUNA,90,JAKAR MAGORI,1,LABARI,2981,NISHADI,282,OSCAR,2,Samaila Yombe,42,SANARWA,31,SHARHI,16,SIYASA,387,TARIHI,11,TSARO,354,WASANNI,18,
ltr
item
ISYAKU.COM: Ni dan fashi da makami ne kawai, bana garkuwa da mutane
Ni dan fashi da makami ne kawai, bana garkuwa da mutane
https://3.bp.blogspot.com/--lgD-eHSWiw/XMNBpbcZCDI/AAAAAAAAVoo/UWyg5RsNiaATivJ_PXC5UwIeCQutvn_PQCLcBGAs/s1600/police5.PNG
https://3.bp.blogspot.com/--lgD-eHSWiw/XMNBpbcZCDI/AAAAAAAAVoo/UWyg5RsNiaATivJ_PXC5UwIeCQutvn_PQCLcBGAs/s72-c/police5.PNG
ISYAKU.COM
https://www.isyaku.com/2019/04/ni-dan-fashi-da-makami-ne-kawai-bana.html
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/2019/04/ni-dan-fashi-da-makami-ne-kawai-bana.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy