Shafin isyaka wapka ya daina aiki, amma isyaku.com ne ya maye gurbinsa

Mujallar ISYAKU.COM na sanar da dimbin masoyanmu masu amfani da karamin shafinmu na ISYAKA WAPKA cewa kampanin WAPKA ya rufe aikace aikacensa har illa masha Allahu daga kasar Ingila. Sakamakon haka ISYAKA.WAPKA.MOBI ya daina aiki kenan, saidai za ku iya samun mu a babban shafinmu na ISYAKU.COM kai tsaye. Akan yi wa ISYAKA WAPKA inkiya da suna SENIORA TECH wanda shi ne kampani na farko da ya fara samar da labarai ta wannan tsari a jihar Kebbi.

Idan baku manta ba, shafin ISYAKA.WAPKA.MOBI na buda shi ne domin samar da dama ga jama'ar mu a jihar Kebbi da kuma wasu sassaa na arewacin Najeriya su sami shiga yanar gizo cikin sauki, ta hanyar yin amfani da kimiyyar shiga yanar gizo na XHTML wataau Extensible Hypertext Markup Language wanda ke nada shafin yanar gizo zuwa dunkulallen sila, kuma yake daidaituwa da kwakwalwar wayar salula musamman kananan wayoyi a lokacin da mai amfani da shi yake shiga yanar gizo.

Idan baku manta ba, wannan tsari da na dora shafin, tare da karin amfani da manhajar Google wajen rage nauyin shafi, ya haifar da farin jinin gaske ga ma'abuta amfani da wannan shafi, domin ko da baka da Data, za ka iya yin amfani da N10 ka karanta Jaridun Najeriya akalla guda 5 matukar ka yi amfani da shafin ISYAKA WAPKA a waccan lokaci.

Sakamakon haka muka sami fiye da mutum Miliyan 7 da suka shiga wannan shafi, wanda haka ya bamu kwarin guiwa na ganin mun yi babban shafi wanda zai ci gashin kansa tare da daukaka har da inganta matsayi da kuma matakin shafin, wanda shi ne ya haifar da shahararren shafin nan na ISYAKU.COM wanda ke amfani da kimiyyar zamani na ANDROID a wayar salula.

Sakamakon haka, ISYAKA.WAPKA.MOBI ya daina aiki, amma za ku iya samun amfanin wannan shafi a ISYAKU.COM, kuma ingantaccen shafi ne da ke dauke da duk Jaridu da irin labaran da kuke samu a tsohon shafin na ISYAKA.WAPKA.MOBI wanda ke amfani da kimiyar wayar salula na JAVA..

Za ku iya rubuta ISYAKU ko ISYAKU.COM a Google, sai ku dannan Nema watau search, Google zai kai ku shafin ISYAKU.COM sai ku nemi labaran da kuke so. Idan kuma kana neman labarin Jaridu ne, sai ka je can kasan shafin ISYAKU.COM mun yi maku tanadin labarai.

DAGA ISYAKU.COM 

 Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM 

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN