Legit Hausa
Dazu nan ne labari yake zuwa mana
cewa wasu dubun wasu Matasa da su ka saba damfarar mutane babu gaira babu
dalili ta hanyar yanar gizo sun shiga hannun jami’an hukumar EFCC a Najeriya.
Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya
ta kama wasu Bayin Allah matasa har 7 da ke amfani da zamba-cikin-aminci wajen
satar dukiyar jama’a, ta hanyar yi masu karya da lambo.
Kamar yadda labari ya zo mana daga
hannun hukumar EFCC da kan-ta, ta hannun jami’an ta, ana zargin wadannan Matasa
da laifin zamba-cikin-aminci, da karya, da yaudara da lambo wajen samun makudan
kudi daga Bayin Allah. EFCC ta bayyana sunayen wadanda aka cafke a yankin Lekki
da Ajah na cikin Garin Legas da; Abdulsalam Toheeb, Salam Sikiru, Abdusalam
Rasaq, Azeez Oladimeji, Eniola Mogaji, Alabi Ridwan da kuma Asoroti Oluwaseun.
Daga cikin kayan da aka karbe a
hannun wadannan Madamfara akwai manyan motoci kirar Honda Crosstour da Toyota
Camry. Jami’an EFCC sun kuma samu na’urori irin su gafaka 7 da manyan wayoyin
salula na zamani har 6. EFCC ta shafin ta na Facebook ta tabbatar da cewa za a
makawa wadannan samari a gaban kotu inda za a tuhume su da laifuffukan da aka
ayyana domin ya zama darasi ga wasu masu wannan aiki.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi