Jami'an EFCC sun damke babbar alkaliya 'Ofili-Ajumogobia' a harabar kotu


Legit Hausa

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta bayyana dalilinta na saka damke korarriyar alkaliyar babbar kotun tarayya, Jastis Rita Ofili-Ajumogobia. A wani jawabi da shugaban sashen yada labarai da sadar wa, Tony Orilade, ya fitar a yau, Talata, EFCC ta ce ta sake kama Ofili-Ajumogobia ne domin samun damar sake shirya wasu sabbin tuhume-tuhume a kan ta. Sanarwar ta kara da cewa, kama Ofili-Ajugomobia, ya biyo bayan wani hukunci da kotun daukaka kara a Legas karkashin Jastis Hyeladzira Nganjiwa ta taba yanke wa a kan cewar, ba za a iya gurfanar da alkali ko alkaliya ba har sai an kore shi daga aiki ko kuma hukumar kula da bangaren shari'a (NJC) tayi masa ritayar dole.

EFCC ta ce ta gurfanar da Jastis Ofili-Ajumogobia a gaban NJC kuma tunda sun dauki mataki a kan ta, yanzu zasu tunkari kotu da sabbin tuhume-tuhume a kan ta. An fara gurfanar da Ofili-Ajumogobia da babban lauyan Najeriya (SAN), Godwin Obla, a ranar 30 ga watan Nuwamba na shekarar 2016 a kan wasu tuhume-tuhume 30 da suka hada da cin hanci, bayar da da bayan karya, tauye hukunci da sauransu. Daga baya hukumar EFCC ta gyara tuhumar da ta ke yi masu daga guda 30 zuwa 31.

Kafin fitar da jawabin na EFCC, Legit.ng ta sanar da ku cewar ana ta tafka takaddama a harabar babbar kotun Ikeja, yayin da jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) suka mamaye kotun domin cafke tsohuwar mai shari'ar a babbar kotun gwamnatin tarayya, Rita Ofili Ajumogobia. Wannan kuwa ya biyo bayan watsi da karar da aka shigar ta laifuka 30 da EFCC ke tuhumar mai shari'a Ajumogibia da aikatawa, gaban mai shari'a Hakeem Oshodi. Ajumogibia na fuskantar tuhuma kan laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa da kuma amfani da ofishinta ta hanyar da ba ta dace ba.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN