Yanzu - yanzu: Barayi sun yi ma wani Limami duka har ya mutu a jihar Jigawa


Legit Hausa

A yau Asabar dinnan ne wasu da ake zargin barayi ne, suka kashe limamin kauyen Kwara, dake karamar hukumar Kiyawa, cikin jihar Jigawa, hukumar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwan lamarin.


Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar, SP Abdu Jinjiri, shine ya fadawa kamfanin dillacin labarai na Najeriya, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 1:30 na dare. Jinjiri ya ce marigayin mai suna, Al-Sheikh Idris Musa, mazaunin garin Kwara, barayin sun kai masa hari a gidansa bayan ya sayar da gonarsa akan kudi naira dubu 400, ga wani kamfanin gine-gine da ke jihar.

Ya ce wadanda ake zargin sun yi ta dukan marigayin da itace, wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa. Jami'in ya kara da cewa wadanda ake zargin sun dauki kudin da marigayin ya sayar da gonar ta sa, naira dubu dari hudu.

A cewarsa, wadanda ake zargin bayan kashe marigayin, sun daki matanshi da 'ya'yanshi. "Ana tsammanin cewa an yi cinikin gonar a gaban wadanda ake zargin, sai dai har yanzu ba a san su waye ba.

"Munn dauki iyalan marigayin da barayin suka daka munn kai su asibiti mafi kusa domin karbar magani," in ji Jinjiri. Ya kara da cewa sun bar gawar marigayin ga iyalanshi domin ayi masa sallah a binne shi. Ya ce, yanzu haka 'yan sanda sun fara gabatar da bincike akan lamarin, kuma za su yi kokari wajen ganin sun kama wadanda ake zargin.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN