Jam’iyyar PDP ta gargadi Malami akan zaben Rivers


Legit Hausa

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta gargadi ministan shari’a, Abubakar Malami, bisa yunkurin hargitsa gudanarwar kiduddugan kuri’un zaben gwamna da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris a jihar Rivers.

Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) ta dakatar da tattara sakamakon zabe saboda rikici da ya mamaye zaben. Hukumar ta kafa ranar 2 zuwa 5 ga watan Afrilu don cigaba da kidudduga don bayyana wanda ya lashe zaben.

A wani jawabin da kakakin PDP Kola Ologbondiyan ya gabatar jiya, yace dole Malami ya tsare kansa kuma kada ya yarda ayi amfani da shi wajen gudanar da ayyukan da suka saba ma doka a harkar da ya shafi zaben Rivers Jam’iyyan ta kara gargadin Malami bisa zargin jawabin da ministan sufuri, Rotimi Amaeci yayi, cewa Malami na aiki don baiwa shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu umurnin, tsayar da tattara sakamakon .

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa anatan jihar Zamfara ta tsakiya, Kabiru Marafa, ya bayyana cewar gwamna Abdulaziz Yari na jihar ta Zamfara ya saba wa Allah a kan hakikicewar da yake yi a kan cewar jam'iyyar APC ta gudanar da zaben fidda 'yan takara a Zamfara.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai a kan harkokin siyasa a jihar Zamfara, Sanata Marafa ya bayyana cewar kamata ya yi gwamna Yari ya nemi yafiyar Allah a kan yaudarar da ya yiwa mutanen jihar Zamafara a kan batun zaben fidda 'yan takara.

 DAGA ISYAKU.COM

 Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN