Fankar jirgi mai saukar Angulu na sojin sama ya fille kan wani soji a Bama

Fankar jirgin sama mai saukar Angulu na mayakan sojin Najeriya ya fille kan wani sojin sama a Bama na jihar Borno ranar Asabar da yamma.

Rahotanni sun ce jirgin ya sami matsala, sakamakon haka wani jami'in sojin sama wanda mai taimaka ma matukin jirgin ne ya je domin ya dauko jakarsa a cikin jirgin. Amma tsautsayi ya sa fankar jirgin ya fille kan wannan soji domin fankaar jirgin yana aiki lokacin da sojin ya shiga jirgin .

Wannan lamari ya faru da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Asabar. An adana gawar mamacin yayin da aka tafi da jirgin sansanin sojin sama.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post