A daidai lokacin da
kashe-kashe suka yi kamari a jihar Zamfara, gwamnatin Tarayya ta sanar
da haramta duk wasu hidimomin hakar ma’adanai a fadin jihar Zamfara,
sannan ta baiwa ‘yan kasashen wajen wa’adin sa’o’i 48 da su gaggauta
ficewa daga yankunan da ake hakar ma’adanan.
Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Muhammad Adamu ne ya
fitar da wannan sanarwa yau Lahadi a fadar Shugaban Kasa a yayin da ya
gana sa manema labarai, a cewarshi wannan yana daga cikin kokarinsu na
kawo karshen barayin Zamfara.
Babban jami’in ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da suke tare da
Shugaban Ma’aikatan fadar gwamnatin Tarayya, Abba Kyari, da darekta
janar na hukumar DSS Yusuf Bichi, da kuma darekta janar na hukumar leken
asiri ta Nijeriya wato NIA, Ambasada Ahmad Rufa’i.
Adamu ya bayyana cewa dakatar da hakar ma’adanan ya biyo bayan rahoton
sirri da hukumomin tsaro suka samu, inda ake zargin masu hakar ma’adanan
suna matukar taimakawa wadannan ‘yan fashi da makamin da suka addabi
jihar Zamfara da sauran jihohi masu makwabtaka da Zamfara din.
Don haka gwamnatin Tarayya ta bada umarni kamar haka; an dakatar da
hakar ma’adanai a jihar Zamfara da ma jihohin kusa da ita, sannan duk
wani mai hakar ma’adanan da ya sake ya haki ma’adanai za a soke lasisin
sa.
Sannan wadanda ba ‘yan asalin Nijeriya bane, an basu sa’o’i 48 su
tattara i-nasu-i-nasu su fice daga yankunan da ake hakar ma’adanan,
sannan jami’an tsaron sun tabbatar wa da al’ummar yankunan da abun yafi
shafa cewar suna iya iyawarsu don ganin sun shawo kan lamarin.
Read More at: https://hausa.leadership.ng/2019/04/07/gwamnatin-tarayya-ta-haramta-hakar-gwal-a-zamfara/
Read More at: https://hausa.leadership.ng/2019/04/07/gwamnatin-tarayya-ta-haramta-hakar-gwal-a-zamfara/
Leadership Hausa
A daidai lokacin da kashe-kashe suka
yi kamari a jihar Zamfara, gwamnatin Tarayya ta sanar da haramta duk wasu
hidimomin hakar ma’adanai a fadin jihar Zamfara, sannan ta baiwa ‘yan kasashen
wajen wa’adin sa’o’i 48 da su gaggauta ficewa daga yankunan da ake hakar
ma’adanan.
Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘yan
sandan Nijeriya, Muhammad Adamu ne ya fitar da wannan sanarwa yau Lahadi a
fadar Shugaban Kasa a yayin da ya gana sa manema labarai, a cewarshi wannan
yana daga cikin kokarinsu na kawo karshen barayin Zamfara.
Babban jami’in ya bayyana hakan ne a
daidai lokacin da suke tare da Shugaban Ma’aikatan fadar gwamnatin Tarayya,
Abba Kyari, da darekta janar na hukumar DSS Yusuf Bichi, da kuma darekta janar
na hukumar leken asiri ta Nijeriya wato NIA, Ambasada Ahmad Rufa’i.
Adamu ya bayyana cewa dakatar da
hakar ma’adanan ya biyo bayan rahoton sirri da hukumomin tsaro suka samu, inda
ake zargin masu hakar ma’adanan suna matukar taimakawa wadannan ‘yan fashi da
makamin da suka addabi jihar Zamfara da sauran jihohi masu makwabtaka da
Zamfara din.
Don haka gwamnatin Tarayya ta bada
umarni kamar haka; an dakatar da hakar ma’adanai a jihar Zamfara da ma jihohin
kusa da ita, sannan duk wani mai hakar ma’adanan da ya sake ya haki ma’adanai
za a soke lasisin sa.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi