• Labaran yau


  An gurfanar da korarren dansanda da ya kashe mutum gaban Kotu sanye da ankwa

  Mafarauci ya zama wanda aka yi farauta,  korarren safeton yansanda Olalekan Ogunyemi wanda ya yi amfani da bindigarsa na aikin dansanda kirar AK47 ya bindige wani matashi har lahira, ya bayya a gaban wata Kotu a birnin Lagos sanye da ankwa.

  Alkalin Kotun Majistare Mrs. A.O. Salawu ta bayar da umarni a tasa keyar Olalekan zuwa Kurkuku har lokacin da za a sami shawara daga ofishin DPP na jihar Lagos.

  Tun farko, mai gabatar da kara na yansanda safeto Kehinde Olatunde ya shaida wa Kotu cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ranar 31 ga watan Maris da misalin karfe 5:10 na yamma, a rukunin gidaje na Onipetesi da ke Idi-Mangoro a jihar Lagos inda ya bindige wani mahaifin yaro daya mai suna Kolade Johnson Kolade.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An gurfanar da korarren dansanda da ya kashe mutum gaban Kotu sanye da ankwa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama