Wani korarren dansanda mai suna Felix Nwogugu ya fada hannun yansanda bisa tuhumar safarar makamai a jihar Abia.
Kwamishinan yansandan jihar Abia Mr. Ene Okon ne ya shaida wa manema labarai haka. Ya ce dubun Felix wanda korarren dansanda ne ta cika bayan wani fashi da makami a jihar.
Ya kara da cewa sakamakon bincike a kan zancen fashi da makamin ne aka bankado cewa korarren dansandan ne ke sayarwa bata gari makamai.
Yansanda na ci gaba da bincike kan lamarin.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi