Tsohon shugaban kasar Peru Alan Garcia ya bindige kanshi har lahira da karamar bindiga kirar Pistol yayain da yansanda suka je gidanshi domin su kamashi bisa tuhumar karbar cin hanci .
An garzaya zuwa Asibiti da Mr Garcia a Lima babban birnin kasar ta Peru inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Yansanda sun isa gidan Mr Garcia ne domin su tafi da shi bisa zargin karbar cin hanci daga wani kampanin kwangila na kasar Brazil Odebrecht, amma sai ya bukaci ya kira wayar salula, ya kuma shiga wani daki ya rufe kofa, daga bisani sai yansanda suka ji karar tashin bindiga.
Jin haka ke da wuya sai yansandan suka balle kofar dakin inda suka tarar da Mr Garcia zaune a kujera da raunin bindiga a kansa.
Shuagaba Martin Vizcarra na kasar ta Peru ne ya tabbatar da mutuwar tsohon shugaban kasar watau Mr Alan Garcia.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi