Type Here to Get Search Results !

An laka min mallakar Kwarangwam kan dan adam domin ni Bafulatani ne - Wani Bafulatani

Yansandan jihar Oyo sun kama wani Bafulatani dan shekara 30 bayan sun sameshi da Kwarangwam na kan dan adam.

Yansandan sun ce an kama wannan mutum mai suna Musa Ahmed mai shekara 30 ne a garin Ogbomosho, amma abokinsa ya tsere.

Rahoton yansanda ya nuna cewa an damke wannan mutum ne yayin da yansanda suka tsayar da motar haya da sue tafe a ciki kuma suka gudanar da bincike bincike.

Amma a nasa jawabin, Musa cewa ya yi  " Na shiga motar zuwa Ogbomosho ne daga garejin Ilesa Baruba a Illorin na jihar Kwara, kuma na zauna kusa da wani fasinja, bayan yansanda sun tsayar da mu sai suka yi binciken jakar kowane daga cikin fasinja, ganin haka ke da wuya sai mai jakar ya arce da gudu kuma yansanda suka bi shi amma suka kasa kamashi. Daga bisani sai suka ce dole na san shi tunda an sami Kwarangwam na kan dan adam a jakarsa. An laka mini wannan laifi ne domin ni kadai ne Bafulatani a cikin motar".

Yansanda sun ce za su gurfanar da Ahmed musa a gaban Kotu.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN