Bikin kamun Kifi a Birnin kebbi, Matsunta sun afka ruwan Dukku cikin dare

An fara gudanar da Su watau bikin kamun Kifi a Ruwan Dukku da ke hanyar Makera, kuma a gefen Dutsen Dukku da ke garin Birnin Kebbbi na jihar Kebbi.


Sai dai an fara bikin ne da misalin karfe 11.00 na dare ranar Laraba 6 ga watan Maris 2019.

Yanzu haka, daruruwan jama'a da suka hada da tsofaffi, matasa da yara daga garin Birnin kebbi da kuma wasu garuruwa sun fara halara kuma an gan motoci dauke da Matsunta suna isowa wannan wuri da aka fara kamun Kifi.

Sai dai an buda ruwan Dukku cikin dare sakamakon yadda jama'a suka afka ma ruwan kamar yadda wata majiya ta shaida mana cewa an bayar da izini ne cewa a shiga ruwan.

Amma wannan yanayi ne mai hadari ganin cewa Matsuntan za su iya cin karo da macizai da sauran halittu da ke boyewa a kasa, ko a cikin ciyawa, hakazalika matsananci sanyi zai iya jawo ma wasu Matsunta lalurar sanyin Awazu ko kirji.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN