Yadda ta kasance a maimaicin zaben Gwamnan jihar Kano


Legit Hausa

Dakta Abdulahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano kuma dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamna, ya sake lashe zabe a karo na biyu bayan an kai ruwa rana tsakaninsa da dan takarar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf.

Ganduje ya lashe zaben ne da banbancin kuri'u 9,000 bayan cike gurbin kuri'un da Abba ya dora masa a zagayen farko na zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris. Sakamakon kananan hukumomi biyu ya kawo tsaiko wajen sanar da sakamakon zaben. Kananan hukumomin su ne; Kibiya da Nasarawa.

A karamar hukumar Kibiya, Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PD ya samu kuri'u 228, yayin da Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 371.

A karamar hukumar Nasarawa, APC ta samu adadain kuri'u 10,536, yayin da jam'iyyar PDP ta samu adadin kuri'u 3,409.

A karshen zaben raba gardama da aka kamma jiya, Asabar, a kananan hukumomi 28, APC ta samu jimillar kuri'u 45,876 da suka ba ta rinjaye a kan jam'iyyar PDP wacce ta samu jimillar kuri'u 10,239.

A zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris, da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewar bai kammalu ba, jam'iyyar PDP ce ke kan gaba da adadin kuri'u 1,014,474, yayin da jam'iyyar APC ke da adadin kuri'u 987,817.

Yanzu bayan an kammala tare da hada jimillar dukkan kuri'un kowacce jam'iyya daga zabukan biyu da aka gudanar, jam'iyyar APC na da kuri'u 1,033,695 da suka ba ta nasara a kan jam'iyyar PDP, wacce ta samu kuri'u 1,024,713.

 DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN