Oshiomhole ya ce mukami daya kacal APC za ta bar wa PDP a majalisa


Legit Hausa

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewar mambobin jam'iyyar sa ne kadai zasu samu mukami a majalisar tarayya in banda kujerar shugaban marasa rinjaye.

Da yake magana yayin wata ganawa da mambobin majalisar wakilai da aka zaba a karkashin tutar jam'iyyar APC, Oshiomhole ya ce APC zata yi amfani da rinjayen da take da shi wajen zabar shugabannin majalisar.

Oshiomhole ya kara da cewar mambobin jam'iyyar APC ne zasu shugabanci kwamitocin majalisar in banda shugabancin kwamitin asusun jama'a, wanda doka ta bayyana cewar na jam'iyyar adawa ne.

An gudanar da taron ne a cibiyar Yar'Adua da ke Abuja, birnin tarayya. "Muna da yawan mambobin da zamu samar da kakakin majalisa, a saboda haka shugaban majalisa dole ya kasance dan jam'iyyar APC. "Ina son ku saka a cikin zukatan ku cewar tamkar 'yan uwan juna mu ke, za mu hada kai kamar yadda alamar tsintsiya ta jam'iyyar mu ke nunua wa.

"Mu na da yawan zamu karbi shugabancin majalisa kuma zamu yi amfani da yawan mu don cimma wannan buri na mu. "Kujerar shugabanci daya ce APC za ta bari; kujerar shugaban marasa rinjaye. Ba zamu raba mukamin shugabancin majalisa da na kwamitoci da wata jm'iyyar ba. Da 'yan Najeriya a son wata jam'iyya ta shugabanci majalisa da sun zabi mambobin jam'iyyar fiye da na jam'iyyar APC," a cewar Oshiomhole.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN