Legit Hausa
Aminu Waziri Tambuwal, dan takarar
gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya samu nasarar yin tazarce a kan
kujerar sa ta gwamnan jihar Sokoto da tazarar kuri’u ma fi kankanta bayan
kamala tattara sakamako daga kananan hukumomi 22 da aka maimaita zabe a jiya,
Asabar.
An tattara tare da sanar da
sakamakon zaben gardama a hedikwatar hukumar zabe ta kasa (INEC) dake garin
Sokoto. A zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris da INEC ta bayyana cewar bai
kammmalu ba, jam’iyyar PDP na da kuri’u 489,558, yayin da jam’iyyar APC da
Ahmad Aliyu ke yiwa takara ta samu kuri’u 486,145.
A wancan lokacin, jam’iyyar PDP a
kan gaba da tazarar kuri’u 3,413 amma saboda soke wasu kuri’u a a akwatinan
zabe 136 dake kananan hukumomi 22 da adadin masu rijistar zabe 75,403, INEC ta
ce sai an je zagaye na biyu domin kece raini kamar yadda doka ta tanada.
A yayin da ya rage saura sakamakon
zabe daga karamar hukumar Kebbe a sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar
Sokoto, jam'iyyar PDP na da jimillar kuri'u Jimilla kuri'u 18342 daga mazabun
da aka maimaita zabe, yayin da APC ke da adadin kuri'u 16987.
A sakamakon zaben karamar hukumar
Kebbe da aka sanar, jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 5,457, yayin da APC ta samu
kuri’u 7,173. A sakamakon zabe na karshe da baturiyar zabe, Farfesa Fatima
Batulu Mukhtar, ta sanar, jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 25,857, yayin da APC ta
samu kuri’u 25,515.
Bayan an kara sakamakon zaben raba
gardamar a kan tsohon sakamakon zaben dake hannun INEC, Aminu Waziri Tambuwal
na jam’iyyar PDP ya samu jimillar kuri’u 512,002, yayin da Ahmad Aliyu na
jam’iyyar APC ya samu jimillar kuri’u 511,661.A saboda haka, jam’iyyar PDP ta
kayar da APC da tazarar kuri’u 341. Tazarar da masu bibiyar lamuran siyasa da
zabe a Najeriya ke ganin ba a taba samun mai kankantar ba a zaben kujerar gwamna.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi