KAI TSAYE: Yadda zaben gwamnan Bauchi zagaye na 2 ke gudana a rumfuna 36


Legit Hausa

A ranar 19 ga watan Maris, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki. Sai dai bayan kammala zaben, hukumar ta sanya sunan jihar Bauchi daga cvikin jihohin da za a sake gudanar da zabe a rumfunan da ba a kammala zabensu ba.

Kamar yadda kwamishinan zabe na jihar Bauchi, Mr Kyari ya bayyana, akwai rumfunan zabe 36 da za a sake gudanar da zabensu a kananan hukumomi 15 na jihar, wanda kuma tuni hukumar ta kammala rarraba kayayyakin zaben, inda har wasu rumfunan ma zaben ya fara gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Legit.ng Hausa ta shirya tsaf, domin kawo maku muhimman bayanai, labarai game da rahotanni kan yadda zaben gwamnan jihar Bauchin zagaye na biyu ke gudana a rumfunan zaben da lamarin ya shafa.

Hakan zai iya zuwa maku walau a labarin cikin hotuna ko kuma labari na zube akan tsarin rahoto. Bisa rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu, har an kammala zabe tare da fara kirga kuri'un da aka kad'a a wasu rumfunan zabe ajihar Bauchi.

Misalin hakan shine karamar hukumar Jama'are, gundumar Mamaheta, rumfar zaben Gidan Jauro. LGA: Kirfi Ward: Bara Central PU: Kofar Sarki/Yaki bara (002) - Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben da aka kammala kadawa. - Da misalin karfe 11 na safiya, rundunar 'yan sanda ta yi kokarin dakile wani yunkuri na satar akwati. -----

Rahoto A jihar Bauchi: Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro na MOPOL, sun hargitsa zabe a gundumar Jama'are da ke karamar hukumar Jama'are, akwati na 010. ----- Rahoto Rahotanni sun bayyana cewa ana ganin kananan yara da basu kai shekaru 18 ba a layin zabe domin kad'a kuri'arsu a karamar hukumar Jama'are, gundumar Jama'are \b\, akwatin zabe na 010 - Jabori, makarantar firamare ta Jabori. ----- LGA: Jamare Ward: Mamaheta PU: Gidan Jauro (020) - An kammala kad'a kuri'a, an fara kirga sakamakon kuri'un da aka kad'a. - Akwai sama da jami'an 'yan sanda guda 20 a rumfar zaben. -----

LGA: DARAZO Ward: Darazo PU: 026 Kofar jauro Bappah Zabe na ci gaba da gudana lami lafiya, kuma akwai jami'an tsaro da ke sa ido. ----- 9:00am - 11:00am: LGA: Jamare PU: Jabbori Primary School Time: 9:53am - Ana ci gaba da kad'a kuri'a - Akwai jami'an tsaro ('yan sanda, hukumar shige da fice) - Na'u'rorin 'Card reader' na amfani lafiya lau. ----- LGA: Toro Ward: Ribina PU: Sala Primary School (019) Time: 9:57 - Ana ci gaba da kad'a kuri'a - Akwai jami'an tsaro ('yan sanda, hukumar shige da fice) - Na'u'rorin 'Card reader' na amfani lafiya lau. ----- Rahoto A jihar Bauchi: A gundumar Bara, rumfar zabe ta 002, karamar hukumar Kirfi. Zafe na ci gaba da gudana lami lafiya bayan fara tantancewa da kad'a kuri'a da misalin karfe 8:45 na safe. -----

Rahoto A rumfar zaben Kagadaman Dass da ke a jihar Bauchi, an samu dan hargisti bayan da wasu 'yan siyasa suka isa wajen. Sai dai, masu kad'a kuri'ar sun fatattake su kuma komai ya dawo dai dai. Yanzu haka dai ana ci gaba da kad'a kuri'a lami lafiya a rumfar zaben. ----- LGA: KIRFI Ward: BARA PU: 002 Time: 10.08am An fara tantancewa da kada kuri'a da misalin karfe 8:45, kuma zaben yana gudana lami lafiya. ----- LGA: Kirfi Ward: Unguwa M. Jakin PU: Kofar Ayuba Time: 9:28am - Ana ci gaba da kad'a kuri'a - Akwai jami'an tsaro ('yan sanda, NSCDC) - Na'u'rorin 'Card reader' na amfani lafiya lau - Akwai wakilan jam'iyya guda 4 ----- LGA: Ajili/Samadawo Ward: Ehaje PU: Ajili Primary Schol. 001 Time: 9:13am - Ana ci gaba da tantancewa da kuma kad'a kuri'a tun wajen karfe 8. - Akwai jami'an tsaro. - Na'u'rorin 'Card reader' na amfani lafiya lau. -----

LGA: Kirfi Ward:Bara Central, Kofar Sarki PU: Yaki Bara (002) - Ana ci gaba da kad'a kuri'a - Akwai jami'an tsaro ('yan sanda, hukumar shige da fice) - Na'u'rorin 'Card reader' na amfani lafiya lau. -----

L.G.A: TORO Ward: RIBINA PU: Salarma primary school 009 Ana ci gaba da kad'a kuri'a. Akwai jami'an tsaro a rumfar zaben. ----- LGA: Shira WARD: Bukul/Bangire PU: Languran, Kofar Sarki (028) Akalla akwai jami'an tsaro guda 20 a rumfar zaben, yayin da wasu 11 suka isa wajen da misalin karfe 8:30 na safiya -----

LGA: Toro WARD: Jama'a/Zaranda PU: 031 An fara tantancewa da kuma kada kuri'a da misalin karfe 8 na safiya. ----- Kafin fara bayyana maku abubuwan da ke wakana, bari mu fara yi maku bita kan yawan mutanen da suka yi rejistar zaben a rumfunan zabe 36 da ke cikin kananan hukumo 15 da aka soke zabensu.

ALKALERI (01) BIRIN/ GIGARA/ YANKARI (07) BARTAK - BARTAK PRIMARY SCHOOL (004) MUTANE: 458 JAMDA - PRIMARY SCHOOL (016) MUTANE: 732 BOGORO (03) BOGORO \D\"" (04) MALLAR GIJI/H., DAJI - MALLAR (008) MUTANE: 1130 DARAZO (05) GABARIN (03) UNGUWAR SARKI, KOFAR FADA GALADIMA (001) MUTANE: 997 LANZAI (07) UNGUWAR FADA, VILLAGE HEAD OFFICE I (001) MUTANE: 1073 TUDUN WADA WARGI, PRIMARY SCHOOL (013) MUTANE: 405 DARAZO (01) GARIN JAURO BAPPAH, KOFAR JAURO BAPPAH (026) MUTANE: 271 DASS (06) DOTT (06) KAGADAMA, KAGADAMA PRIMARY SCHOOL (004) MUTANE: 872 GAMAWA (07) ZINDI (11) GARIN JAURO SHEHU, SHEHU VILLAGE (012) MUTANE: 405 GANJUWA (08) KARIYA (04) HAKA TAFI, KOFAR SARKI (010) MUTANE: 462 MIYA WEST (08) JILI, KOFAR SARKI (020) MUTANE: 844 GIADE (09) UZUM \B\"" (08) FAGUJI CENTRE, PRIMARY SCHOOL II (003) MUTANE: 328 ZIRRAMI (10) ZIRAMI, PRIMARY SCHOOL (003) MUTANE: 473 DOGUWA CENTRAL (03) GULBUM, KOFAR SARKI (007) MUTANE: 552 U. ZUM \A\"" (07) GADAULE, KOFAR JAURO (005) MUTANE: 546 ITAS/GADAU (10) ITAS (01) UNGUWAR MATI, MAGAMA ITAS (003) MUTANE: 1033 JANKUDE, BAKIN RIJIYA (015) MUTANE: 388 ITAS KOFAR FADA, DISTRICT HEAD OFFICE 023) MUTANE: 831 JAMAARE (11) JAMA'ARE \B\"" (02) JABBORI, JABBORI PRIMARY SCHOOL (010) MUTANE: 524 HANAFARI (08) MAMAHETA, GIDAN JAURO (020) MUTANE: 305 KATAGUN (12) MADARA (04) DUNARI, KOFAR JAURO (009) MUTANE: 333 MADANGALA (03) DUHUWA, KOFAR JAURO (011) MUTANE: 989 CHARACHARA PRIMARY SCH, PRIMARY SCHOOL (013) MUTANE: 733 KIRFI (13) DEWU EAST (06) WURO GUMBAL, KOFAR SARKI (006) MUTANE: 294 BARA (02) BARA CENTRAL, KOFAR SARKI/YAKI BARA (002) MUTANE: 817 MISAU (14) AJILIN/GUGULIN (05) AJILI/SAMADAWO, AJILI PRIMARY SCHOOL (001) MUTANE: 1007 NINGI (15) JANGU (04) BAURE, KOFAR MAI UNGUWA (013) MUTANE: 692 NASARU (03) ZAZIKAI, I, KOFAR MAI UNGUWA (005) MUTANE: 350 HARDO LAGGA, KOFAR HARDO LAGGA (007) MUTANE: 335 SAMA (09) KWANGI I, KWANGI PRIMARY SCHOOL (018) MUTANE: 530 TIFFI / GUDA (07) UNGUWAR M. JAKIN, KOFAR AYUBA (018) MUTANE: 626 SHIRA (16) BUKUL/BANGIRE (03) LANGURAN, KOFAR SARKI (028) MUTANE: 438 TORO (18) RIBINA (03) SALAMA, PRIMARY SCHOOL (019) MUTANE: 908 JAMA'A / ZARANDA (06) ZULL PRY. SCH. (031) MUTANE: 940 TAMA (10) GURUNGU, KOFAR SARKI (014) MUTANE: 522 ZUNA I, KOFAR SARKI (018) MUTANE: 498 TOTAL 29 RAs 36 PUs 22,641

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN